Jeremiah 19:11 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
ka kuma ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa zan farfasa wannan al’umma da wannan birni kamar yadda aka farfasa wannan tulu mai ginin tukwane ba kuwa zai gyaru ba. Za a binne matattu a Tofet har sai ba sauran wuri.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَاكَثٜىٰ مُسُ، ‹إِنْجِنِ يَهْوٜىٰهْ مَيْ ضُنْدُنَا ، حَكَ ذَنْ ڢَشٜىٰ مُتَنٜىٰنْ بِرْنِنَّنْ، كَمَرْ يَدَّ مُتُمْ يَكَنْ ڢَشٜىٰ تُلُنْ دَ مَيْ غِنِنْ تُݣُونٜىٰ يَغِنَ، يَدَّ بَذَيْسَاكٜىٰ ڠَرُبَ؞ ذَاعَبِنّٜىٰ مُتَنٜىٰ أَ تُواْڢٜىٰتْ حَرْ سَيْ وُرِنْ بِنّٜىٰوَ يَكَاسَ؞ نِے يَهْوٜىٰهْ نَا ڢَطَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
ka kuwa ce musu, ‘Ubangiji Mai Runduna ya ce, haka zai farfasa jama'a, da wannan birni kamar yadda aka fashe tulun maginin tukwanen, ba kuwa zai gyaru ba. Za a binne mutane a Tofet domin za a rasa makabartar da za a binne su.