Jeremiah 19:4 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Gama sun yashe ni suka kuma mai da wannan wuri ya zama na baƙin alloli; sun ƙone hadayu a cikinsa wa allolin da ko su ko kakanninsu ko sarakunan Yahuda ba su taɓa sani ba, suka kuma cika wannan wuri da jini marasa laifi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَمَا مُتَنٜىٰنَّنْ سُنْ رَبُ دَنِے، سُنْ ڧَظَنْتَرْدَ وُرِنَّنْ تَوُرِنْ ڧُواْنَ وَ غُمَكَ تُرَارٜىٰ، غَ أَلُّواْلِنْ دَ كُواْ سُو، كُواْ كَاكَنِّنْسُ، كُواْ سَرَاكُنَنْسُ نَ يَهُودَ مَا بَسُ سَنِبَ؞ سُنْ ثِكَ وَنَّنْ وُرِے دَ جِنِنْ مَرَسَ لَيْڢِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ga shi, mutanen nan sun rabu da ni, sun ƙazantar da wannan wuri sun ƙona wa gumaka turare, waɗanda su, ko kakanninsu, ko sarakunan Yahuza, ba su san su ba. Sun cika wannan wuri da jinin marasa laifi.