Jeremiah 19:5 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Suka gina masujadai na kan tudu na Ba’al don su ƙona ’ya’yansu maza a cikin wuta a matsayin hadaya ga Ba’al abin da ban umarta ba, ban ambata ba, bai kuma zo mini ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سُنْ كُمَ غِنَا وُرَارٜىٰنْ سُجَّدَ غَ بَعَلْ دُواْمِنْ سُمِيڧَ مَسَ یَیَنْسُ هَدَايَ تَڧُواْنَاوَا ثِكِنْ وُتَا، أَبِنْدَ بَنْ عُمَرْتَبَ، بَنْ ڢَطَا بَ، بَنْ مَايِ تُنَانِنْسَبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sun gina wa Ba'al masujadai don su miƙa masa 'ya'yansu maza hadayar ƙonawa, abin da ban umarta ba, ban kuma ba da izni ba, ban ma yi tunanin haka ba.