Jeremiah 2:11 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Akwai wata al’ummar da ta canja allolinta? (Duk da haka su ba alloli ba ne sam.) Amma mutanena sun musayar da ɗaukakarsu da gumakan banza.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كُواْ أَݣَويْ وَتَ أَلْعُمَّرْ دَ تَتَٻَ ثَنْجَ أَلُّواْلِنْتَ، كُواْدَيَكٜىٰ سُو بَ أَلُّواْلِبَنٜىٰ؟ عَمَّا جَمَعَتَ سُنْ ثَنْجَ نِے دَ نَكٜىٰ طَوْكَكَرْسُ دَ غُمَكَ مَرَسَ أَمْڢَانِ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Akwai wata al'umma da ta taɓa sāke gumakanta Ko da yake su ba kome ba ne? Amma mutanena sun sauya darajarsu da abin da ba shi da rai.