Jeremiah 2:13 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Mutanena sun aikata zunubai guda biyu. Sun rabu da ni, ni da nake maɓulɓular ruwan rai, sun kuma haƙa tankunan ruwansu, tankuna ruwan da suka fashe da ba za su iya riƙe ruwa ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَمَا مُتَنٜىٰنَ سُنْ عَيْكَتَ مُغُنْتَا إِرِ بِيُ، سُنْڧِينِ، نِے دَ نَكٜىٰ مَٻُٻُّغَرْ ضُوَ مَيْ بَادَ رَيْ؞ سُنْ حَڧَ وَكَنْسُ تَڢْكُنَنْ ضُوَ، تَڢْكُنَنْ دَسُكٜىٰ أَڟَڟَّٰغُ، بَسُ عِيَ رِڧٜىٰ ضُوَبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Mutanena sun yi zunubi iri biyu, Sun rabu da ni, ni da nake maɓuɓɓugar ruwan rai, Sun haƙa wa kansu tafkunan ruwa, hudaddu, Waɗanda ba za su iya ajiye ruwa ba.