Jeremiah 2:25 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kada ka yi gudu har ƙafafunka su zama ba takalma maƙogwaronka kuma ya bushe. Amma sai ka ce, ‘Ba amfani! Ina ƙaunar baƙin alloli kuma dole in bi su.’
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كٜىٰ إِسْرَٰٓءِيلَ، كَدَ كِغُدُ حَرْ تَاكَلْمَنْ ڧَڢَاڢُنْكِ سُثِنْيٜىٰ، حَرْ مَڧُواْڠُورُوانْكِ يَبُوشٜىٰ سَبُواْدَ بِنْ وَطَنْسُ أَلُّواْلِ؞ عَمَّا كِنْ ثٜىٰ، ‹إِنَا! بَذَنْ عِيَ دَيْنَ بِنْسُبَ! غَمَا إِنَ سُوانْسُ، سُو كُوَ ذَنْبِے!›
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kai Isra'ila, kada ka bar ƙafafunka ba takalma, Kada kuma ka bar maƙogwaronka ya bushe. Amma ka ce, ‘Wannan ba amfani, Gama na ƙaunaci baƙi, su kuwa zan bi.’