Jeremiah 2:8 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Firistoci ba su yi tambaya, ‘Ina Ubangiji ba.’ Waɗanda suke amfani da doka ba su san ni ba; shugabanni suka yi mini tawaye. Annabawa suka yi annabci ta wurin Ba’al, suna bin gumakan banza.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ڢِرِسْتُواْثِے بَسُ تَمْبَيِ جُونَبَ ثٜىٰوَ ‹إِنَا نٜىٰ يَهْوٜىٰهْ يَكٜىٰ؟› مَاسُ لُورَ دَ كُواْيَرْوَرْ مُوسَٰى بَسُ سَنِّبَ؞ مَكِيَايَنْ مُتَنٜىٰنَ سُنْيِ مِنِ تَاوَيٜىٰ، أَنَّبَاوَا سُنْيِ أَنَّبْثِ دَ سُونَنْ بَعَلْ، سُنْبِے غُمَكَ مَرَسَ أَمْڢَانِ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Firistoci kuma ba su ce, ‘Ina Ubangiji Yake?’ ba. Masanan shari'a ba su san ni ba. Masu mulki sun yi mini laifi, Annabawa sun yi annabci da sunan Ba'al, Sun bi waɗansu abubuwa marasa amfani.”