Jeremiah 20:15 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
La’ananne ne mutumin da ya kawo wa mahaifina labari, wanda ya sa shi ya yi murna cewa, “An haifa maka yaro, ɗa namiji!”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
لَعَنَنّٜىٰ نٜىٰ مُتُمِنْ دَ يَكَيْ لَابَرِنْ حَيْڢُوَتَ غَ بَابَنَ، وَنْدَ يَسَا بَابَنَ يَيِ مُرْنَ دَ ثٜىٰوَ «أَنْ حَيْڢَ مَكَ طَا!»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
La'ananne ne mutum da ya kai wa mahaifina labari Cewa, “An haifa maka ɗa,” don ya sa shi farin ciki.