Jeremiah 20:4 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Gama ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Zan maishe ka abin razana ga kanka da kuma ga dukan abokanka; da idanunka za ka gan takobin abokan gāba yana kashe su. Zan miƙa Yahuda duka ga sarkin Babilon, wanda zai kwashe su zuwa Babilon ya kuma kashe su da takobi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَمَا إِنْجِ يَهْوٜىٰهْ ، ‹غَاشِ، ذَنْ مَيْشٜىٰكَ أَبِنْ ڟُواْرُواْ غَ كَنْكَ دَ دُكَنْ أَبُواْكَنْكَ؞ أَعِدُوانْكَ، أَبُواْكَنْ غَابَا ذَاسُ كَشٜىٰ أَبُواْكَنْكَ دَ تَكُواْبِے؞ ذَنْ بَادَ مُتَنٜىٰنْ يَهُودَ أَ حَنُّنْ سَرْكِنْ بَابِيلَ، ذَيْ كُوَ ݣُوشٜىٰسُ ذُوَا بَوْتَا عَ بَابِيلَ عِنْدَ ذَيْ كَشٜىٰسُ دَ تَكُواْبِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Haka Ubangiji ya ce, ‘Ga shi, zan maishe ka abin tsoro ga kai kanka, da dukan abokanka. Abokan gābansu za su kashe su da takobi a kan idonka. Zan ba da dukan Yahuza a hannun Sarkin Babila, shi kuwa zai kwashe waɗansu ya kai bautar talala a Babila, ya kuma kashe waɗansu da takobi.