Jeremiah 20:7 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ya Ubangiji, ka ruɗe ni, na kuwa ruɗu; ka fi ni ƙarfi, ka kuwa yi nasara. Na zama abin dariya dukan yini; kowa yana yi mini ba’a.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَا يَهْوٜىٰهْ ، كَرُوطٜىٰنِ، نَاكُوَ رُوطُ؞ كَڢِينِ ڧَرْڢِے، كَكُوَ شَا كَيْنَ؞ نَذَمَ أَبِنْ دَارِيَا دُكَنْ يِنِ، كُواْوَ يَنَ تَيِمِنِ بَعَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Ya Ubangiji ka ruɗe ni, na kuwa ruɗu, Ka fi ni ƙarfi, ka kuwa rinjaye ni. Na zama abin dariya dukan yini, Kowa yana ta yi mini ba'a.