Jeremiah 21:10 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Na ƙudura in yi wa wannan birni lahani ba alheri ba, in ji Ubangiji. Za a ba da shi a hannuwan sarki Babilon, zai kuwa hallaka shi da wuta.’
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَمَا نِے يَهْوٜىٰهْ نَا طَوْرَ ڢُسْكَ تَيِنْ غَابَادَ بِرْنِنَّنْ دُواْمِنْ إِنْكَٰوُاْ مَسَ مَسِيڢَ بَ أَلْحٜىٰرِبَ؞ ذَنْ بَادَشِ غَ سَرْكِنْ بَابِيلَ، شِيكُوَ ذَيْ ڧُواْنَشِ دَ وُتَا؞ نِے يَهْوٜىٰهْ نَا ڢَطَا؞› »
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Gama na ƙudura zan kawo wa wannan birni masifa, ba alheri ba. Zan bashe shi a hannun Sarkin Babila, shi kuwa zai ƙone shi da wuta.’ ”