Jeremiah 22:28 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Wannan mutum Yehohiyacin ne da aka rena, fasasshen tukunya, abin da babu wanda yake so? Me ya sa za a jefar da shi da ’ya’yansa a jefar da su a ƙasar da ba su sani ba?
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَيَ كُواْنِيَ يَذَمَ كَمَرْ ڢَسَشّٜىٰنْ تُلُ، تُلُنْ دَ بَاوَنْدَ يَكٜىٰسُوانْسَ؟ مٜىٰيَسَا عَكَ جٜىٰڢَرْ دَشِ دَ یَیَنْسَ عَڧَسَرْدَ بَسُ سَنِبَ؟
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ashe, Yekoniya kamar fasasshen tulu yake, Wanda ba wanda ya kula da shi? Me ya sa aka watsar da shi da 'ya'yansa, A ƙasar da ba su sani ba?