Jeremiah 23:17 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Suna cin gaba da ce wa waɗanda suka rena ni, ‘ Ubangiji ya ce za ku zauna lafiya.’ Ga duka waɗanda suke bin taurin zukatansu kuwa sukan ce, ‘Babu lahanin da zai same ku.’
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَنَّبَاوَنَّنْ سُنَ تَڢَطَا وَمَاسُ رٜىٰنَ مَغَنَرْ يَهْوٜىٰهْ ، ‹أَيْ، ذَاكُ ذَوْنَ لَاڢِيَ!› سُنَ تَڢَطَا وَمَاسُ تَڢِيَ ثِكِنْ تَوْرِنْ ذُوثِيَارْسُ، ‹بَابُ مَسِيڢَرْ دَ ذَاتَ ذُواْ مُكُ!›
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Suna ta faɗa wa waɗanda suke raina maganar Ubangiji cewa, ‘Za ku zauna lafiya!’ Ga kowane mai bin nufin tattaurar zuciyarsa, ‘Ba masifar da za ta same ka.’ ”