Jeremiah 23:26 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Har yaushe wannan zai ci gaba a cikin zukata annabawa masu ƙarya, waɗanda suke annabcin ruɗun tunaninsu?
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
حَرْ يَوْشٜىٰ ڧَضْيَا ذَاتَ ڢِتَ دَغَ ذُوثِيَارْ أَنَّبَاوَنَّنْ مَاسُ ڧَضْيَا؟ حَرْ يَوْشٜىٰ أَنَّبَاوَنَّنْ ذَاسُيِتَيِ أَنَّبْثِنْ رُوطُنْ دَيَكٜىٰ أَ ذُوثِيَارْسُ؟
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Har yaushe ƙarya za ta fita daga zuciyar annabawan nan masu annabcin ƙarya, waɗanda suke annabcin ruɗin da yake a zuciyarsu?