Jeremiah 24:2 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kwando guda yana da ’ya’yan ɓaure masu kyau sosai, kamar waɗanda suka nuna da wuri; ɗayan kwandon kuma yana da ’ya’yan ɓaure marasa kyau, sun yi muni har ba a iya ci.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَثِكِنْ ݣُونْدُواْ طَيَ أَݣَويْ ٻَوْرٜىٰ مَاسُ ݣَوْ، كَمَرْ نَنُونً ڢَارِ؞ عَثِكِنْ طَيَنْ كُوَ مَرَسَ ݣَوْنٜىٰ، وَطَنْدَ بَعَ عِيَ ثِنْسُ سَبُواْدَ رَشِنْ ݣَنْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A ɗaya kwandon akwai ɓaure masu kyau, kamar nunan fari. A ɗayan kuwa marasa kyau ne, ba mai iya cinsu.