Jeremiah 24:8 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“ ‘Amma kamar ’ya’yan ɓauren nan marasa kyau, waɗanda sun yi muni har ba a iya ci,’ in ji Ubangiji, ‘haka zan yi da Zedekiya sarkin Yahuda, fadawansa da sauran mutanen da suka tsira a Urushalima, ko suna a wannan ƙasa ko suna zama a Masar.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«عَمَّا كَمَرْ يَدَّ ٻَوْرٜىٰ مَرَسَ ݣَوْ سُنْ ضُٻَ يَدَّ بَعَ عِيَ ثِنْسُ سَبُواْدَ رَشِنْ ݣَنْسُ، حَكَ ذَنْ مَيْدَ سَرْكِے صَدِڧِيَ نَ يَهُودَ دَ دَتَّاوَنْسَ دَ ضَغُواْوَرْ مُتَنٜىٰنْ عُرُوشَلِيمَ وَطَنْدَ سُكَ ضَغٜىٰ عَڧَسَرْ نَنْ دَ كُمَ وَطَنْدَ سُكَ تَڢِے ڧَسَرْ مَصَرْ؞ نِے يَهْوٜىٰهْ نَا ڢَطَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Ni Ubangiji na ce, zan mai da Zadakiya Sarkin Yahuza, da sarakunansa, da sauran mutanen Urushalima da suka ragu a ƙasar, da mutanen da suka tafi Masar, kamar ruɓaɓɓen ɓauren nan da suka lalace har ba su ciwuwa.