Jeremiah 25:15 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya faɗa mini, “Ka karɓi kwaf ruwan inabin nan na fushina a wurina, ka sa dukan al’umman da na aike ka gare su, su sha.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَا مَغَنَرْ دَ يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نَ إِسْرَٰٓءِيلَ يَڢَطَا مِنِ «إِرْمِيَ، ڢُشِنَ يَنَ كَمَرْ ضُوً إِنَبِے عَثِكِنْ ݣُوڢْ؞ كَكَرْٻٜىٰشِ دَغَ هَنُّونَ، كَسَا دُكَنْ أَلْعُمَّنْ دَ ذَنْ عَيْكٜىٰكَ وُرِنْسُ، سُشَا ݣُوڢْ نَڢُشِنَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ubangiji Allah na Isra'ila ya ce mini, “Ka karɓi ƙoƙon ruwan inabin nan na fushina a wurina, ka sa dukan al'umman da na aike ka gare su, su sha.