Jeremiah 25:19 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Fir’auna sarkin Masar, ma’aikatansa, fadawansa da dukan mutanensa,
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
نَكُمَبَا سَرْكِے ڢِرْعَوْنَ نَ مَصَرْ دَ مَاسُ يِمَسَ حِدِمَ دَ دَتَّاوَنْسَ دَ دُكَنْ مُتَنٜىٰنْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ga lissafin sauran da za su sha ƙoƙon. Fir'auna Sarkin Masar da kuma barorinsa, da sarakunansa, Dukan jama'arsa, da dukan baƙin da suke tare da su, dukan sarakunan ƙasar Uz, dukan sarakunan ƙasar Filistiyawa, wato Ashkelon, da Gaza, da Ekron, da saura na Ashdod, Edom da Mowab, da 'ya'yan Ammon maza, dukan sarakunan Taya, da dukan sarakunan Sidon, dukan sarakunan da suke gaɓar Bahar Rum da waɗanda suke a tsibiran tekun, Dedan, da Tema, da Buz, da dukan waɗanda suke yi wa kansu sanƙo, dukan sarakunan Arabiya, dukan sarakunan tattarmukan mutane da suke zaune a hamada, dukan sarakunan Zimri, da dukan sarakunan Elam, da dukan sarakunan Mediya, dukan sarakunan arewa, na nesa da na kusa bi da bi. Dukan mulkokin da suke fuskar duniya za su sha daga ciki. Daga nan sai Sarkin Babila a bayansu duka, zai sha nasa.