Jeremiah 25:3 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Shekaru ashirin da uku, daga shekara ta goma sha uku ta Yosiya ɗan Amon sarkin Yahuda har zuwa wannan rana, maganar Ubangiji ta zo mini na kuma yi muku magana sau da sau, amma ba ku saurara ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«تُنْدَغَ شٜىٰكَرَا تَغُواْمَشَا عُكُ تَمُلْكٍ سَرْكِے يُواْسِيَا طَنْ أَمُوانْ نَ يَهُودَ، يَهْوٜىٰهْ يَا يِتَيِنْ مَغَنَ دَنِے عَكَيْ عَكَيْ، وَتُواْ شٜىٰكَرَا عَشِرِنْ دَ عُكُ كٜىٰنَنْ؞ نِے ڢَا إِنَ تَڢَطَا مُكُ كُلُّمْ، عَمَّا بَ كُجِبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Shekaru ashirin da uku ke nan tun daga shekara ta goma sha uku ta mulkin Yosiya, ɗan Amon, Sarkin Yahuza, har zuwa yau, Ubangiji ya yi mini magana, ni kuwa na yi ta faɗa muku, amma ba ku ji ba.