Jeremiah 25:30 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Yanzu ka yi annabcin dukan waɗannan maganganu a kansu ka kuma ce musu, “ ‘ Ubangiji zai yi ruri daga bisa; zai yi tsawa daga mazauninsa mai tsarki ya kuma yi ruri da ƙarfi a kan ƙasarsa. Zai yi ihu kamar waɗanda suke matsin ’ya’yan inabi, yi ihu a kan dukan waɗanda suke zaune a duniya.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«كَيْ، إِرْمِيَ، سَيْكَيِ أَنَّبْثِنْ دُكَنْ وَطَنَّنْ كَلْمُواْمِ غَابَادَسُو؞ كَڢَطَا مُسُ، « ‹ يَهْوٜىٰهْ ذَيْ يِ رُورِ دَغَ ثَنْ سَمَ، مُرْيَرْسَ ذَاتَ ڢِتُواْ دَغَ وُرِنْ ذَمَنْسَ مَيْ ڟَرْكِے؞ ذَيْ يِ رُورِنْ ڢُشِنْسَ عَكَنْ غَرْكٜىٰنْسَ، ذَيْ يِ إِيهُ كَمَرْ مَاسُ تَتَّاكَ یَیَنْ إِنَبِے دُواْمِنْ سُسَامِ ضُوَنْسُ؞ ذَيْ يِ إِيهُ عَكَنْ دُكَنْ مَذَوْنَنْ دُونِيَا،
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Kai Irmiya kuma sai ka yi annabcin dukan waɗannan magana gāba da su, ka faɗa musu cewa, ‘Ubangiji zai yi ruri daga Sama, Zai yi magana daga wurin zamansa mai tsarki, Zai yi wa garkensa ruri da ƙarfi ƙwarai, Zai yi ihu kamar masu matse 'ya'yan inabi, Zai yi gāba da dukan mazaunan duniya.