Jeremiah 25:34 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ku yi kuka ku kuma yi makoki, ku makiyaya; ku yi ta birgima a ƙura, ku shugabannin garke. Gama lokacin da za a yanka ku ya zo; za ku fāɗi ku kuma farfasa kamar tukunyar yumɓu mai kyau.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«كُيِ كُوكَا دَ إِيهُ، يَا كُو مَكِيَايَ، كُيِ بِرْغِمَ عَتُواْكَ، يَا كُو شُوغَبَنِّنْ غَرْكٜىٰنَ؞ غَمَا لُواْكَثِنْ دَ ذَاعَ يَنْكَاكُ يَيِ؞ ذَاكُ ڢَاطِ كُڢَرْڢَشٜىٰ كَمَرْ ݣُونُوانْ ڢَاطِكَمُتُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Ku yi makoki, ku yi kuka, ku makiyaya, Ku yi ta birgima a cikin toka ku iyayengijin garke, Gama ranar da za a yanka ku da ranar da za a warwatsa ku ta zo, Za ku fāɗi kamar zaɓaɓɓen kasko.