Jeremiah 26:18 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Mika mutumin Moreshet, ya yi annabci a kwanakin Hezekiya sarkin Yahuda. Ya ce wa dukan mutanen Yahuda, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “ ‘Za a nome Sihiyona kamar gona, Urushalima kuwa za tă zama tsibin juji, ƙwanƙolin dutsen haikali kuwa zai zama kurmi.’
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«أَنَّبِے مِيكَ دَغَ مُواْرٜىٰشٜىٰتْ يَيِ أَنَّبْثِنْسَ أَ لُواْكَثِنْ دَ سَرْكِے هٜىٰزٜىٰكِيَ يَكٜىٰ مُلْكِ أَ يَهُودَ؞ مِيكَ يَيِ وَدُكَنْ جَمَعَرْ يَهُودَ مَغَنَ ثٜىٰوَ « ‹إِنْجِنِ يَهْوٜىٰهْ مَيْ ضُنْدُنَا ، سِهِيُواْنَ ذَاعَ نُواْمٜىٰتَ كَمَرْ ڢِيلِنْ غُواْنَ، عُرُوشَلِيمَ ذَاتَ ذَمَ تُلِنْ بُواْلَ، تُدُنْ دَ عَكَ غِنَا غِدَنْ يَهْوٜىٰهْ عَكَنْسَ ذَيْ ذَمَ ڧَرَمِنْ وُرِنْ سُجَّدَ عَكُرْمِ؞› »
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Mika kuwa, mutumin Moreshet, ya yi annabci a kwanakin Hezekiya, Sarkin Yahuza, ya faɗa wa dukan mutanen Yahuza cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Runduna ya ce, Za a nome Sihiyona kamar gona, Urushalima kuwa za ta zama tsibin juji, Ƙwanƙolin dutsen Haikalin zai zama kurmi.’