Jeremiah 26:23 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Suka dawo da Uriya daga Masar suka kawo shi wurin Sarki Yehohiyakim, wanda ya kashe shi da takobi aka kuma jefar da gawarsa a makabartar talakawa.)
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سُكَ كَامَ عُرِيَ سُكَ كَٰوُاْ شِ وُرِنْ سَرْكِے يٜىٰهُواْيَكِمْ؞ سَرْكِے يَسَا عَكَ كَشٜىٰشِ دَ تَكُواْبِے، عَكَ كُمَ جٜىٰڢَرْ دَ غَاوَرْسَ أَوُرِنْ بِنّٜىٰ تَلَكَاوَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Suka kamo Uriya daga Masar suka kawo shi wurin sarki Yehoyakim, sai ya sa aka kashe shi da takobi, aka binne gawarsa a makabartar talakawa.