Jeremiah 27:13 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Me ya sa kai da mutanenka za ku mutu saboda takobi, yunwa da annoba waɗanda Ubangiji ya yi barazana wa duk al’ummar da ba za tă bauta wa sarkin Babilon ba?
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُوانْمٜىٰ كَيْ دَ مُتَنٜىٰنْكَ ذَاكُ مُتُ تَوُرِنْ تَكُواْبِے دَ يُنْوَ دَ بَلَعِ، كَمَرْ يَدَّ يَهْوٜىٰهْ يَڢَطَا ذَيْ ڢَرُ دَ كُواْوَثٜىٰ أَلْعُمَّرْ دَ تَڧِے تَبَوْتَاوَ سَرْكِنْ بَابِيلَ؟
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Don me kai da mutanenka za ku mutu ta takobi, da yunwa, da annoba, kamar yadda Ubangiji ya yi magana a kan kowace al'umma da ta ƙi ta bauta wa Sarkin Babila?