Jeremiah 27:16 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai na ce wa firistoci da dukan waɗannan mutane, “Ga abin da Ubangiji yana cewa, kada ku saurari annabawan da suke cewa, ‘Ba daɗewa ba za a komo da kayan gidan Ubangiji daga Babilon.’ Suna muku annabcin ƙarya ne.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَنَ غَمَيِنْ مَغَنَ دَ سَرْكِے، سَيْ نِے إِرْمِيَ نَتَڢِے نَيِ مَغَنَ دَ ڢِرِسْتُواْثِے دَ دُكَنْ جَمَعَ ثٜىٰوَ «إِنْجِنِ يَهْوٜىٰهْ ، كَدَ كُسَوْرَرِ أَنَّبَاوَنَّنْ وَطَنْدَ سُكٜىٰثٜىٰوَ ‹بَ دَ جِمَاوَا بَ، ذَاعَ دَاوُاْ دَ دُكَنْ كَايَنْ دَ عَكَ ݣُوشٜىٰ دَغَ غِدَنْ يَهْوٜىٰهْ ذُوَا بَابِيلَ؞› أَنَّبْثِنْ ڧَضْيَانٜىٰ سُكٜىٰيِ مُكُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan na faɗa wa firistoci da jama'a cewa, “In ji Ubangiji, kada ku kasa kunne ga abin da annabawanku suke muku annabci cewa, ‘Ba da daɗewa ba za a komo da kayan Haikalin Ubangiji daga Babila.’ Ƙarya ce suke yi muku.