Jeremiah 27:18 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
In su annabawa ne da gaske suna kuma da maganar Ubangiji, bari su roƙi Ubangiji Maɗaukaki ya sa kada a kwashe kayayyakin da suka ragu a gidan Ubangiji da kuma a cikin fadar sarkin Yahuda da kuma cikin Urushalima a kai Babilon.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عِدَنْ دَ غَسْكٜىٰنٜىٰ سُو أَنَّبَاوَا مَاسُ سَڧُوانْ يَهْوٜىٰهْ نٜىٰ، تُواْ، بَرِ سُضُواْڧِ يَهْوٜىٰهْ مَيْ ضُنْدُنَا عَكَنْ كَايَنْدَ سُكَ ضَغٜىٰ عَثِكِنْ غِدَنْ يَهْوٜىٰهْ دَ ثِكِنْ غِدَنْ سَرْكِنْ يَهُودَ دَ كُمَ ثِكِنْ بِرْنِنْ عُرُوشَلِيمَ، دُواْمِنْ كَدَ عَتَڢِے دَسُو بَابِيلَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Idan su annabawa ne, idan kuwa Ubangiji yana magana da su, to, bari su roƙi Ubangiji Mai Runduna kada a tafi Babila da kayayyakin da suka ragu a Haikalin Ubangiji, da a fādar Sarkin Yahuza, da a Urushalima.