Jeremiah 27:6 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yanzu zan ba da dukan ƙasashenku ga bawana Nebukadnezzar sarkin Babilon; zan sa namun jeji ma su bauta masa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَنْذُ نَبَادَ دُكَنْ ڧَسَاشٜىٰنَّنْ أَ حَنُّنْ بَاوَنَ سَرْكِے نٜىٰبُكَدْنٜىٰزَّرْ نَ بَابِيلَ، حَرْ مَا نَمُواْمِنْ دَاجِ سُبَوْتَا مَسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Yanzu fa na ba bawana Nebukadnezzar, Sarkin Babila, dukan ƙasashen nan, na kuma ba shi namomin jeji su bauta masa.