Jeremiah 29:1 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ga abin da yake cikin wasiƙar annabi Irmiya da ya aika daga Urushalima zuwa ga sauran dattawan da suka ragu a cikin masu zaman bauta da kuma zuwa ga firistoci, annabawa da kuma dukan sauran mutanen da Nebukadnezzar ya kwashe zuwa zaman bauta daga Urushalima zuwa Babilon.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَا كَلْمُواْمِنْ وَسِيڧَرْ دَ أَنَّبِے إِرْمِيَ يَعَيْكَ دَغَ عُرُوشَلِيمَ، ذُوَاغَ ضَغُواْوَرْ دَتَّاوَنْ جَمَعَرْ يَهُودَاوَا دَ ڢِرِسْتُواْثِے دَ أَنَّبَاوَا دَ دُكَنْ مُتَنٜىٰنْ دَ نٜىٰبُكَدْنٜىٰزَّرْ يَݣُوشٜىٰ دَغَ عُرُوشَلِيمَ ذُوَا بَوْتَا عَ بَابِيلَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ga maganar wasiƙar da annabi Irmiya ya aika daga Urushalima zuwa ga dattawa, da firistoci, da annabawa, da dukan mutanen da Nebukadnezzar ya kwaso daga Urushalima zuwa Babila. (