Jeremiah 29:14 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Za ku same ni,” in ji Ubangiji, “zan kuma komo da ku daga bauta. Zan tattaro ku daga dukan al’ummai in sa ku inda na kore ku,” in ji Ubangiji, “zan kuma komo da ku zuwa wurin da na kwashe ku zuwa zaman bauta.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَنْ كُوَسَا كُسَامٜىٰنِ؞ ذَنْ مَيَرْ مُكُ دَ أَلْبَرْكُنْكُ، إِنْ تَتَّارُواْكُ دَغَ ثِكِنْ دُكَنْ أَلْعُمَّيْ دَ دُكَنْ وُرَارٜىٰ عِنْدَ نَكُواْرٜىٰكُ، نِے يَهْوٜىٰهْ نَا ڢَطَا؞ ذَنْ دَاوُاْ دَكُو أَوُرِنَّنْ دَغَ عِنْدَ نَسَا عَكْوَاشٜىٰكُ ذُوَا ذَمَنْ بَوْتَا؞ نِے يَهْوٜىٰهْ نَا ڢَطَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Za ku same ni, ni Ubangiji na faɗa, zan mayar muku da arzikinku, in tattaro ku daga cikin dukan al'ummai da dukan wurare inda na kora ku, ni Ubangiji na faɗa, zan komo da ku a wurin da na sa a kwashe ku a kai ku zaman talala.’