Jeremiah 3:13 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ki dai yarda da laifinki kin yi wa Ubangiji Allahnki tawaye, kin watsar da alheranki ga baƙin alloli a ƙarƙashin kowane itace mai duhuwa, ba ki kuwa yi mini biyayya ba,’ ” in ji Ubangiji.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كٜىٰ دَيْ كِيَرْدَ دَ لَيْڢِنْكِ ثٜىٰوَ كِنْيِ وَ يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نْكِ ذُنُوبِنْ غَنْغَنْثِ، كِنْ وَاڟَرْدَ مُتُنْثِنْكِ غَ وَطَنْسُ أَلُّواْلِ عَڧَرْڧَشِنْ كُواْوَنٜىٰ إِتَاثٜىٰ مَيْ بَادَ إِنُوَ؞ كِكَڧِ يِنْ بِيَيَّ دَ مُرْيَتَ؞ نِے يَهْوٜىٰهْ نَا ڢَطَا؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ke dai ki yarda da laifinki, Da kika yi wa Ubangiji Allahnki, Kin kuma watsar da mutuncinki a wurin baƙi A gindin kowane itace mai duhuwa. Kika ƙi yin biyayya da maganata, Ni, Ubangiji, na faɗa.