Jeremiah 3:16 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A kwanakin, sa’ad da kuka ƙaru sosai a ƙasar,” in ji Ubangiji, “mutane ba za su ƙara yin magana a kan, ‘Akwatin alkawarin Ubangiji ba.’ Ba zai ƙara shiga zuciyarsu ko su tuna ba; ko su bukace shi, ko kuwa su yi wani irinsa ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
إِنْجِ يَهْوٜىٰهْ «سَعَدَّ كُكَ ڧَارُ كُكَ كُمَ يَلْوَتَ عَڧَسَرْ، عَݣُونَكِنْنَنْ بَذَاعَ ڧَارَيِ مَغَنَ غَمٜىٰدَ عَݣُوتِنْ يَرْجٜىٰجٜىٰنِيَرْ يَهْوٜىٰهْ بَ؞ بَذَاعَ ڧَارَ يِنْ تُنَانِنْسَبَ، بَذَاعَ تُنَ دَشِ، كُواْ أَ نٜىٰمٜىٰشِ، كُواْ كُوَ أَ سَاكٜىٰيِنْ وَنِبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'ad da kuka yawaita a ƙasar, mutane ba za su ƙara yin magana a kan akwatin alkawari na Ubangiji ba. Ba za su ƙara yin tunaninsa ko su tuna da shi, ko su bukace shi, ko kuwa su yi wani irinsa ba.