Jeremiah 3:2 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Ta da idanu ki duba tsaunuka ki gani. Akwai wani wurin da ba a kwana da ke ba? A gefen hanya kin zauna kina jiran masoyanki, kin zauna kamar makiyayi a hamada. Kin ƙazantar da ƙasar da karuwancinki da muguntarki.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«تَادَ عِدَنُونْكِ، يَا كٜىٰ إِسْرَٰٓءِيلَ، كِدُوبَ تُدَّيْ مَرَرْ ثِيَوَ كِغَنِ! أَݣَويْ عِنْدَ بَاكِ ݣُونْتَ كِنْيِ كَارُوَنْثِبَ؟ أَݣَويْ عِنْدَ بَاكِ تَادَ وُرَارٜىٰنْ سُجَّدَبَ؟ كِنْ ذَوْنَ عَبَاكِنْ حَنْيَ كِنَ جِرَا مَسُواْيَنْكِ؞ كَمَرْ مُتُمِنْ أَرَبِيَ، كِنَ ݣُونْتُوانْ ٻَوْنَ أَدَاجِ؞ دَ كَارُوَنْثِنْكِ دَ مُغُنْتَارْكِ، كِنْ ڧَظَنْتَرْدَ ڧَسَرْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ki ta da idonki, ki duba filayen tuddai ki gani, Akwai wurin da ba ki laɓe kin yi karuwanci ba? Kin yi ta jiran abokan sha'anin karuwancinki a kan hanya, Kamar Balaraben da yake fako a hamada. Kin ƙazantar da ƙasar da mugun karuwancinki.