Jeremiah 3:8 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Na ba wa Isra’ila marar bangaskiya takardar saki na kuwa kore ta saboda duk zinanta. Duk da haka na ga cewa ’yar’uwarta marar amincin nan Yahuda ba ta da tsoro; ita ma ta fita ta yi zina.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَهُودَ تَغَ ثٜىٰوَ نَسَكِ إِسْرَٰٓءِيلَ مَرَرْ أَمِنْثِنَّنْ نٜىٰ، سَبُواْدَ تَجُويَا دَغَ غَرٜىٰنِ تَيِ كَارُوَنْثِ؞ عَمَّا دُكْدَهَكَ، یَرْعُوَرْتَ يَهُودَ مَيْ ثِنْ أَمَانَرْ نَنْ، بَتَجِڟُواْرُواْ بَ، عِتَمَا تَتَڢِے تَيِ نَاتَ كَارُوَنْثِنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Yahuza kuwa ta ga dukan karuwancin da marar amincin nan, Isra'ila ta yi, na sake ta, na ba ta takardar sarki. Amma duk da haka maƙaryaciyar 'yar'uwan nan tata, Yahuza, ba ta ji tsoro ba, amma ita ma ta tafi ta yi karuwanci.