Jeremiah 30:16 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“ ‘Amma duk wanda ya cinye ku za a cinye shi; dukan abokan gābanku za su tafi zaman bauta. Waɗanda suka washe ku su ma za a washe su; dukan waɗanda suka mai da ku ganima su ma zan mai da su ganima.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«عَمَّا دُكْ وَطَنْدَ سُكَ ثِنْيٜىٰكِ، سُو مَا ذَاعَ ثِنْيٜىٰسُ؞ دُكَنْ مَاسُ ڧِنْكِ، كُواْوَنّٜىٰنْسُ ذَاسُ تَڢِے بَوْتَا، دُكْ وَطَنْدَ سُكَ ڨُوثٜىٰ كَايَنْكِ، سُو مَا ذَاعَ ڨُوثٜىٰ نَاسُ؞ دُكْ وَطَنْدَ سُكَ ڢَرَوْثٜىٰكِ، سُو مَا ذَاعَ ڢَرَوْثٜىٰسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Domin haka dukan waɗanda suka cinye ku, za a cinye su, Dukan maƙiyanku, kowane ɗayansu zai tafi bauta, Waɗanda suka washe ku, za a washe su. Dukan waɗanda suka kwashe ku ganima, su ma za a kwashe su ganima.