Jeremiah 31:12 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Za su zo su yi sowa don farin ciki a ƙwanƙolin Sihiyona; za su yi farin ciki cikin yalwar Ubangiji hatsi, sabon ruwan inabi da mai, ’ya’yan garken tumaki da na shanu. Za su zama kamar gonar da aka yi wa banruwa, ba za su ƙara yin baƙin ciki ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَاسُذُواْ سُرٜىٰرَ وَاڧَا دَ ڧَرْڢِے، عَكَنْ بَبَّنْ تُدُنْ سِهِيُواْنَ، ڢُسْكَرْسُ ذَاسُيِ حَصْكٜىٰ سَبُواْدَ ڢَضٍ ثِكِ، سَبُواْدَ يَوَنْ أَلْحٜىٰرِنْ يَهْوٜىٰهْ ، أَلْحٜىٰرِ نَݣَوْتَرْ حَڟِ، دَ نَضُوً إِنَبِے دَ نَمَنْ ظَيْتُنْ، دَ نَیَیَنْ تُمَكِ دَ نَیَیَنْ شَانُو؞ رَايُوَرْسُ ذَاتَ ذَمَ كَمَرْ غُواْنَ مَيْ سَامُنْ إِسَشّٜىٰنْ ضُوَ، بَذَاسُ ڧَارَ يَنْڨُونٜىٰبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Za su zo su raira waƙa da ƙarfi, A bisa ƙwanƙolin Sihiyona, Za su yi annuri saboda alherin Ubangiji, Saboda hatsi, da ruwan inabi, da mai, Saboda 'ya'yan tumaki da na shanu. Rayuwarsu za ta zama kamar lambu, Ba za su ƙara yin yaushi ba.