Jeremiah 31:20 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Efraim ba ƙaunataccen ɗana ba ne, ɗan da nake jin daɗinsa? Ko da yake sau da dama ina maganar gāba a kansa, duk da haka nakan tuna da shi. Saboda haka zuciyata tana marmarinsa; ina da jinƙai mai girma dominsa,” in ji Ubangiji.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«أَشٜىٰ، إِڢْرَيِمْ بَڧَوْنَتَثّٜىٰنْ طَا أَغَرٜىٰنِبَ؟ أَشٜىٰ، بَشِ نَكٜىٰجِنْ دَاطِنْسَبَ؟ كُواْدَيَكٜىٰ نَيِ تَيِنْ مَغَنَ غَابَادَشِ، دُكْدَهَكَ، ثِكِنْ ڧَوْنَ نَكَنْ تُنَ دَشِ؞ سَبُواْدَ حَكَ ذُوثِيَاتَ تَنَ مَرْمَرِنْسَ كُلُّمْ، حَڧِيڧَ ذَنْجِے تَوْسَيِنْسَ؞ نِے يَهْوٜىٰهْ نَا ڢَطَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ashe, Ifraimu ba ƙaunataccen ɗana ba ne? Ashe, shi ba ɗan gaban goshina ba ne? A duk lokacin da na ambace shi a kan muguntarsa Nakan tuna da shi da ƙauna. Saboda na ƙwallafa zuciyata a kansa, Hakika zan yi masa jinƙai, ni Ubangiji na faɗa.”