Jeremiah 31:35 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ga abin da Ubangiji yana cewa, shi da ya kafa rana don tă yi haske a yini shi da ya sa wata da taurari su yi haske da dare, shi da yake dama teku don raƙuman ruwansa su yi ruri Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
إِنْجِ يَهْوٜىٰهْ ، شِے وَنْدَ يَكَڢَ رَانَ دُواْمِنْ تَذَمَ حَصْكٜىٰ غَ يِنِ، شِے وَنْدَ يَسَا وَتَ دَ تَوْرَرِ دُواْمِنْ سُذَمَ حَصْكٜىٰ غَ دَرٜىٰ، شِے وَنْدَ يَكَنْ تَادَ تٜىٰكُ حَرْ رَاڧُمَنْ ضُوَ سُيِ هَوْكَ سُيِ رُورِ، شِے وَنْدَ سُونَنْسَ يَهْوٜىٰهْ مَيْ ضُنْدُنَا نٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Haka Ubangiji ya ce, Shi wanda ya ba da rana ta haskaka yini, Ya sa wata da taurari su ba da haske da dare, Shi ne yakan dama teku, ya sa raƙumanta su yi ruri, Sunansa Ubangiji Mai Runduna.