Jeremiah 31:8 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ga shi, zan kawo su daga ƙasar arewa in tattara su daga iyakar duniya. A cikinsu makafi da guragu za su kasance, mata masu ciki da matan da suke naƙuda; jama’a mai yawan gaske za su komo.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَاشِ، ذَنْ كَٰوُاْسُ دَغَ ڧَسَرْ أَرٜىٰوَ، ذَنْ تَتَّرَاسُ دَغَ إِيَاكَرْ دُونِيَا، دُكْ تَرٜىٰدَ مَكَڢِ دَ غُرَغُ، دَ مَثٜىٰ مَيْ ثِكِ، دَ مَثٜىٰنْ دَتَكٜىٰ ثِكِنْ نَڧُدَ، دُكَ ثِكِنْ بَبَّرْ ڧُنْ‌غِيَ، ذَاسُ دَاوُاْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ga shi, zan fito da su daga ƙasar arewa, Zan tattaro su daga manisantan wurare na duniya, Tare da su makafi da guragu, Da mace mai goyo da mai naƙuda, Za su komo nan a babbar ƙungiya.