Jeremiah 32:30 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Mutanen Isra’ila da na Yahuda ba abin da suka yi sai mugunta a gabana daga ƙuruciyarsu; tabbatacce, mutanen Isra’ila ba su yi kome ba sai dai tsokane ni da abin da hannuwansu suka yi, in ji Ubangiji.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
حَڧِيڧَ، تُنْ عَڧُرُثِيَرْسُ، مُتَنٜىٰنْ إِسْرَٰٓءِيلَ دَ نَ يَهُودَ بَسُ عَيْكَتَ كُواْمٜىٰ أَغَبَنَبَ سَيْ مُغُنْتَا؞ بَا أَبِنْدَ سُكَيِ، سَيْدَيْ سُنْسَا نَيِ ڢُشِے تَوُرِنْ أَيُّكَنْ حَنُّوَنْسُ؞ نِے يَهْوٜىٰهْ نَا ڢَطَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Gama jama'ar Isra'ila da ta Yahuza, tun daga ƙuruciyarsu, ba su aikata kome a gabana ba sai mugunta, ba abin da jama'ar Isra'ila suka yi, sai tsokanata da gumaka don in yi fushi da ayyukan hannuwansu, ni Ubangiji na faɗa.