Jeremiah 32:35 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sun gina masujadai kan tudu wa Ba’al a Kwarin Ben Hinnom don su miƙa ’ya’yansu maza da mata hadaya ga Molek, ko da yake ban taɓa umarce su ba, bai kuma zo mini cewa su yi abin banƙyama irin wannan ba ta haka suka sa Yahuda ya yi zunubi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سُكَ كُمَ غِغِّنَ وُرَارٜىٰنْ سُجَّدَ دُواْمِنْ بَعَلْ أَ ݣُورِنْ طَنْ هِنُّوامْ، دُواْمِنْ سُمِيڧَ یَیَنْسُ مَظَا دَ مَاتَا هَدَايَ غَ غُنْكِنَّنْ مُواْلٜىٰكْ؞ نِے كُوَ بَنْ عُمَرْثٜىٰسُ سُيِ حَكَبَ، بَنْ مَا يِتُنَانِنْ إِرِنْ وَنَّنْ أَبِنْ بَنْ ڨَمَبَ؞ تَهَكَ يَهُودَ تَيِ ذُنُوبِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sun gina wa Ba'al masujadai a kwarin ɗan Hinnom don su miƙa 'ya'yansu mata da maza hadaya ga Molek, ni kuwa ban umarce su ba, ba shi kuwa a tunanina. Ga shi, sun aikata wannan abin banƙyama, don su sa Yahuza ta yi zunubi.”