Jeremiah 32:4 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Zedekiya sarkin Yahuda ba zai kuɓuta daga hannuwan Babiloniyawa ba amma tabbatacce za a ba da shi ga sarkin Babilon, zai kuwa yi masa magana fuska da fuska ya kuma gan shi da idanunsa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَرْكِے صَدِڧِيَ نَ يَهُودَ بَذَيْ ڟِيرَا دَغَ حَنُّنْ كَلْدِيَاوَا بَ، عَمَّا لَلَّيْ ذَاعَ بَادَشِ أَ حَنُّنْ سَرْكِنْ بَابِيلَ؞ ذَيْ يِمَغَنَ دَ سَرْكِنْ بَابِيلَ ڢُسْكَ دَ ڢُسْكَ، يَكُمَ غَنْشِ عِدُواْ دَ عِدُواْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Zadakiya Sarkin Yahuza kuwa, ba zai tsere wa Kaldiyawa ba, amma za a ba da shi a hannun Sarkin Babila. Zai yi magana da shi fuska da fuska, ya kuma gan shi ido da ido.