Jeremiah 32:7 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Hananel ɗan Shallum ɗan’uwan mahaifinka zai zo wurinka ya ce, ‘Saya filina a Anatot, domin a matsayinka na dangi na kurkusa hakkinka ne kuma kai ya wajaba ka saye shi.’
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَاشِ، هَنَمٜىٰلْ طَنْ شَلُّمْ، طَنْعُوَنْ بَابَنْكَ، يَنَ ذُوَا وُرِنْكَ؞ ذَيْذُواْ يَثٜىٰ مَكَ، ‹سَيَ وَكَنْكَ غُواْنَتَ وَدَّ تَكٜىٰ أَعَنَتُواتْ، غَمَا تُنْدَيَكٜىٰ كَيْنٜىٰ مَڢِے كُسَ ثِكِنْ دَنْغِ كَنَدَ حَكِّ كَڢَنْشِ غُواْنَرْ سَيْ كَسَيَ؞›
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
ga shi, Hanamel, ɗan Shallum kawuna, zai zo wurina ya ce mini, ‘Ka sayi gonata wadda take a Anatot, gama kai ne ka cancanci ka fanshe ta, sai ka saye ta.’ ”