Jeremiah 32:8 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Sa’an nan, kamar dai yadda Ubangiji ya faɗa, sai ga Hananel yaron ɗan’uwan mahaifina ya zo wurina a sansanin matsara ya ce, ‘Saya filina a Anatot a yankin Benyamin. Da yake hakkinka ne ka fanshe shi ka kuma mallake shi, ka sayo shi wa kanka.’ “Sai na gane cewa wannan maganar Ubangiji ce;
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بِسَغَ مَغَنَرْ يَهْوٜىٰهْ ، سَيْ هَنَمٜىٰلْ، طَنْ طَنْعُوَنْ بَابَنَ، يَذُواْ وُرِينَ أَ عِنْدَ عَكَ كُلّٜىٰنِ أَ ڢِيلِ نَغٜىٰڢٜىٰنْ مَاسُ غَادِ؞ يَثٜىٰ مِنِ، ‹سَيِ غُواْنَتَ وَدَّ تَكٜىٰ أَعَنَتُواتْ عَيَنْكِنْ بِلِيَامِنُ، غَمَا كَيْنٜىٰ مَڢِے كُسَ ثِكِ دَنْغِ كَنَ كُمَ دَ حَكِّ كَڢَنْشِ غُواْنَرْ؞ سَيِ غُواْنَرْ دُواْمِنْ كَنْكَ؞› تَهَكَ نَسَنِ وَنَّنْ مَغَنَرْ يَهْوٜىٰهْ ثٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Hanamel ɗan kawuna ya zo wurina a gidan waƙafi, bisa ga faɗar Ubangiji, ya ce mini, “Ka sayi gonata wadda take a Anatot a ƙasar Biliyaminu, gama kai ne ka cancanta ka mallake ta, kai ne za ka fanshe ta, sai ka saye ta.” Sa'an nan na sani wannan maganar Ubangiji ce.