Jeremiah 33:11 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
sowa ta farin ciki da murna, muryoyin amarya da na ango, da muryoyin waɗanda suka kawo hadayun salama a gidan Ubangiji suna cewa, “ ‘ “Ku yi godiya ga Ubangiji Maɗaukaki, gama Ubangiji mai alheri ne; ƙaunarsa za tă dawwama har abada.” Gama zan mayar da wadatar ƙasar kamar yadda suke a dā,’ in ji Ubangiji.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مُرْيَرْ مُرْنَ دَ تَڢَضٍ ثِكِ دَ مُرْيَرْ أَنْغُواْ دَ تَأَمَرْيَ، دَ مُرْيُواْيِنْ مَاسُ رٜىٰرَ وَاڧَا يَايِنْ دَسُكٜىٰ كَٰوُاْ ݣَوْتَيْ نَنُونَ غُواْدِيَ سُنَ ثٜىٰوَ « ‹كُيِ غُواْدِيَ غَ يَهْوٜىٰهْ مَيْ ضُنْدُنَا ، غَمَا يَهْوٜىٰهْ مَيْ أَلْحٜىٰرِ نٜىٰ، ڧَوْنَرْسَ مَرَرْ ثَنْجَاوَا تَهَرْ أَبَدَاثٜىٰ!› «ذَاسُ ڢَطِ حَكَ غَمَا ذَنْ مَيَرْ وَ ڧَسَرْدَ أَلْبَرْكُنْتَ كَمَرْ يَدَّ تَكٜىٰ أَدَا؞ نِے يَهْوٜىٰهْ نَا ڢَطَا؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
za a sāke jin muryar murna da ta farin ciki, da muryar ango da ta amarya, da muryoyin mawaƙa, sa'ad da suke kawo hadayun godiya a cikin Haikalin Ubangiji, suna cewa, ‘Ku yi godiya ga Ubangiji Mai Runduna, Gama Ubangiji nagari ne, Gama madawwamiyar ƙaunarsa tabbatacciya ce.’ Gama zan mayar da arzikin ƙasar kamar yadda yake a dā, ni Ubangiji na faɗa.”