Jeremiah 33:12 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, ‘A wannan wuri, kango da babu mutane ko dabbobi, cikin dukan garuruwansa za a sāke kasance da wurin kiwo don makiyaya su hutar da garkunansu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
إِنْجِ يَهْوٜىٰهْ مَيْ ضُنْدُنَا «يَنْذُ وَنَّنْ وُرِے يَذَمَ كُڢَيْ، بَابُ مُتُمْ كُواْ دَبَّ عَثِكِ؞ عَمَّا أَوُرِنَّنْ دَ كُمَ ثِكِنْ دُكَنْ غَرُرُوَنْسَ، ذَاعَ سَاكٜىٰ سَامُنْ ڢِيلَيٜىٰنْ كِيوُاْ عِنْدَ مَكِيَايَ ذَاسُ ذَوْنَ تَرٜىٰدَ غَرْكُنَنْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Haka Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Wannan wuri wanda yake kufai, inda ba mutum ko dabba, da cikin dukan biranensa, zai sāke zama makiyaya, inda masu kiwo za su zauna da garkunansu.