Jeremiah 33:24 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Ba ka lura ba cewa waɗannan mutane suna cewa, ‘ Ubangiji ya ƙi masarautai biyu da ya zaɓa’? Saboda haka suka rena mutanena ba sa ƙara ɗaukansu a matsayin al’umma.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«بَكَجِ أَبِنْدَ جَمَعَرْ نَنْ سُكٜىٰ ڢَطِ بَ؟ سُنَ ثٜىٰوَ ‹غِدَنَّنْ بِيُ إِسْرَٰٓءِيلَ دَ يَهُودَ وَطَنْدَ يَهْوٜىٰهْ يَذَاٻَا، أَيْ، يَڧِسُ!› تَهَكَ سُكَ رٜىٰنَ جَمَعَتَ، بَسُ طَوْكٜىٰسُ أَلْعُمَّبَ كُمَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Ba ka ji abin da mutanen nan suke cewa ba? Wai, ‘Ubangiji ya ƙi iyalin nan biyu da ya zaɓa!’ Suka raina jama'ata, ba su kuma maishe ta al'umma ba.