Jeremiah 34:1 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yayinda Nebukadnezzar sarkin Babilon da dukan sojojinsa da kuma dukan mulkokinsa da mutanen masarautar da yake mulki suna yaƙi da Urushalima da dukan garuruwan da suke kewaye, sai wannan magana ta zo wa Irmiya daga wurin Ubangiji cewa,
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَا مَغَنَرْ دَ يَهْوٜىٰهْ يَيِ وَ إِرْمِيَ، سَعَدَّ سَرْكِے نٜىٰبُكَدْنٜىٰزَّرْ نَ بَابِيلَ دَ دُكَنْ سُواْجُواْجِنْسَ دَ سُواْجُواْجِنْ دُكَنْ مُلْكُواْكِنْ أَلْعُمَّنْ دَسُكٜىٰ عَڧَرْڧَشِنْسَ دَ كُمَ دُكَنْ ڧَبِيلُ سُنَ يَاڧِ دَ عُرُوشَلِيمَ دَ دُكَنْ غَرُرُوَنْتَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ubangiji ya yi magana da Irmiya sa'ad da Nebukadnezzar, Sarkin Babila, da dukan sojojinsa, da dukan sojojin mulkokin al'umman da suke a ƙarƙashinsa, da dukan mutane suke yaƙi da Urushalima da dukan biranenta.