Jeremiah 34:10 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka dukan fadawa da mutane suka yi yarjejjeniyar cewa za su ’yantar da bayinsu maza da mata ba za su kuwa ƙara riƙe su bayi ba. Suka yarda, suka kuma sake su.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُكَنْ دَتَّاوَا دَ دُكَنْ مُتَنٜىٰنْ دَ سُكَيِ يَرْجٜىٰجٜىٰنِيَ ثٜىٰوَ كُواْوَ ذَيْ سَكِ بَايِنْسَ مَظَا دَ مَاتَا، دُكَنْسُ سُكَيِ بِيَيَّ سُكَ یَنْتَرْ دَسُو؞ بَ كُوَ ذَاسُ ڧَارَ سَاسُ سُيِ مُسُ بَوْتَبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai suka yi biyayya. Dukan sarakuna da dukan jama'a waɗanda suka yi alkawarin, cewa kowa zai 'yantar da bawansa ko baiwarsa, ba za su ƙara bautar da su ba, suka yi biyayya, suka 'yantar da su.