Jeremiah 34:15 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Bai daɗe ba da kuka tuba, kuka kuma yi abin da yake mai kyau a idona. Kowannenku ya yi shelar ’yanci ga ɗan’uwansa. Kun ma yi yarjejjeniya a gabana a gidan da ake kira da Sunana.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَعَدَطٜىٰبَ دَكُكَ تُوبَ، كُواْوَنّٜىٰنْكُ يَيِ أَبِنْدَ يَكٜىٰ دَيْدَيْ أَغَبَنَ تَوُرِنْ يِنْ شٜىٰلَرْ یَنْثِ غَ جُونَنْكُ، كُكَ كُمَيِ يَرْجٜىٰجٜىٰنِيَ أَغَبَنَ أَ غِدَنْ دَ عَكٜىٰ كِرَا دَ سُونَنَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A 'yan kwanakin da suka wuce kuka yi abu mai kyau a gabana da kuka tuba, har kuka yi wa juna shelar 'yanci. Kuka yi alkawari a gabana a Haikalin da ake kira da sunana.