Jeremiah 34:17 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Saboda haka, ga abin da Ubangiji yana cewa, kun yi mini rashin biyayya; ba ku yi shelar ’yanci don ’yan’uwanku ba. Saboda haka yanzu na yi muku shelar ’yanci in ji Ubangiji, ’yanci ga mutuwa ta takobi, annoba da kuma yunwa. Zan sa ku zama abin ƙyama ga sauran mulkokin duniya.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«حَڧِيڧَ، إِنْجِنِ يَهْوٜىٰهْ ، بَ كُيِ مِنِ بِيَيَّ تَوُرِنْ شٜىٰلَرْ یَنْثِبَ، كُواْوَنّٜىٰنْكُ غَ مَڨُوبْثِنْسَ؞ دُواْمِنْ حَكَ، غَاشِ، إِنَيِمُكُ شٜىٰلَرْ یَنْثِ، یَنْثِنْ مُتُوَ تَوُرِنْ تَكُواْبِے دَ بَلَعِ دَ يُنْوَ؞ ذَنْسَا كُذَمَ أَبِنْ ڟُواْرُواْ غَ دُكَنْ مُلْكُواْكِنْ دُونِيَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Domin haka ni Ubangiji na ce, ba biyayya kuka yi mini ba, da irin shelar 'yancin da kowannenku ya yi wa ɗan'uwansa da maƙwabcinsa, saboda haka ni zan yi muku shelar 'yanci zuwa mutuwa ta takobi, da annoba, da yunwa. Zan sa ku zama abin ƙyama ga dukan mulkokin duniya.